Wani 'Da ya kashe Mahaifinsa mai shekaru 83 a duniya a jihar Enugu

Wani 'Da ya kashe Mahaifinsa mai shekaru 83 a duniya a jihar Enugu

A wani sabon rahoto da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya, mun samu cewa hukumar 'yan sandan jihar Enugu ta fara gudanar da bincike kan kisan wani Mahaifi mai shekaru 83 da ya afku a yankin Ojinato na jihar dake Kudancin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, ana zargin dan dattijon da ya riga mu gidan gaskiya da aikata wannan ta'addanci a doron kasa.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, SP Ebere Amaraizu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai da cewar lamarin ya afku ne a ranar 4 ga Mayu.

Wani 'Da ya kashe Mahaifinsa mai shekaru 83 a duniya a jihar Enugu

Wani 'Da ya kashe Mahaifinsa mai shekaru 83 a duniya a jihar Enugu

A rahoton da Kakakin ya bayyana, kawowa yanzu ba bu ainihin sunan wannan yaro da ake zargi da aika-aikan, sai dai ya bayar da tabbacin cewa bincike na nan ya ci gaba da kankama domin bankado gaskiyar dake cikin lamarin.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Mataimakin Shugaban kasa ya halarci taron jam'iyyar sa ta APC a Mazabar sa

Legit.ng ta fahimci cewa,Nathaniel Chukwuemerie, dattijon mai shekaru 83 a duniya da ajali ya katsewa hanzari haifaffen garin Odimi dake karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra, inda dan sa ya yi amfani da tabarya wajen rade ma sa kai da har ya ce ga garin ku nan.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, a yayin garzayawa da dattijon zuwa babban asibitin Orji River likitoci suka tabbatar da cikawar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel