APC zata haramtawa wasu 'ya'yan ta takarar gwamna

APC zata haramtawa wasu 'ya'yan ta takarar gwamna

Uwar jam'iyyar APC ta ce ta kammala shiri tsaf domin haramtawa wasu 'ya'yan jam'iyyar yin takarar gwamna a jihar Ekiti.

Jam'iyyar na wadannan kalamai ne biyo bayan samun hargitsin da aka samu a wurin taron fitar da dan takarar gwamna da jam'iyyar ta gudanar a karshen makon jiya.

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanar da haka jiya, Litinin, a shelkwatar jam'iyyar dake Abuja.

APC zata haramtawa wasu 'ya'yan ta takarar gwamna

APC zata haramtawa wasu 'ya'yan ta takarar gwamna

Bolaji na wadannan kalamai ne bayan jam'iyyar ta karbi rahoton kwamitin gwamna Tanko Al-Makura da jam'iyyar ta dorawa alhakin gudanar da zaben fitar da dan takarar.

DUBA WANNAN: An kama wata dalibar jami'a na kokarin cusa jaririn da ta haifa cikin masai

A cewar Bolaji, shugabancin jam'iyyar zai zauna a daren jiya, Litinin, domin tattauna matakin da zata dauka a kan abinda ya faru tare da daukan alkawarin sanar da jama'a, yau, Talata.

Saidai sakataren yada labaran bai ambaci sunayen 'yan takarar da jam'iyyar zata haramtawa takarar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel