Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Keyamo da wasu 6 a matsayin mambobin hukumar NDIC

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Keyamo da wasu 6 a matsayin mambobin hukumar NDIC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mista Festus Keyamo da wasu mutane shida a matsayin mambobin hukumar Nigeria Deposit Insurance Corporation, NDIC.

Keyamo zai wakilci jihar Delta a hukumar.

Shugaban majaisar dattawa, Bukola Saraki ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisa a ranar Talata inda yake neman yardarm yan majalisan domin tabbatar da nade-naden.

KU KARANTA KUMA: Lauya a jihar Legas ta siyo sababbin wukake don ta kashe mijinta – ‘Yan Sanda

Idan bazaku manta ba a kawanan ne ministan sufuri, Mista Rotimi Ameachi wanda ya zamo jagoran yakin neman zaben Buhari ya nada Keyamo a matsayin kakakin kungiyar neman zaben Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel