Babu wani sauran gari da ke hannun Boko Haram: Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya

Babu wani sauran gari da ke hannun Boko Haram: Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya

Najeriya ta shaidawa Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York cewa a halin yanzu babu wani yanki na kasar da ke hannun mayakan Boko Haram kamar yadda ya faru a shekarun baya lokacin da yan kungiyar suka kwace kananan hukumomi 14 a jihar Borno.

Jakadan Najeriya a majalisar, Samson Itegboje, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke gabatar da sakon Najeriya a babban taron da aka gudanar a kan hadin kai da samar da dawamamen zaman lafiya a hedkwatan hukumar.

Babu wani yankin Najeriya da ke hannun Boko Haram: Gwamnati ga Majalisar Dinkin Duniya

Babu wani yankin Najeriya da ke hannun Boko Haram: Gwamnati ga Majalisar Dinkin Duniya

Itegboje ya ce an kira taron ne a lokacin da kasashen duniya ke fama da fitintunu iri daban-daban da suka hada da rikicin iyakokin kasashe, matsalar bakin haure, hari ta yanar gizo, dumaman yanayi da ta'adanci.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ne ya ceto Najeriya daga rugujewa - Keyamo

"Nigeria kamar sauran kasashen tana fama da wasu daga cikin matsalolin. A shekarun baya, kungiyar Boko Haram sun kwace kananan hukumomi 14 a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

"Sai dai bayan hawan mulki da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a 2015, shugaban kasan ya tabbatar da cewa an kwato dukkan garuruwan da 'yan ta'addan suka kwace. A halin yanzu, babu wani gari da ke karkashin ikon yan kungiyar na Boko Haram," inji shi.

Itegboje ya ce Najeriya zata cigaba da bayar da gudunmawa ga kasashen wajen samar da zaman lafiya da kuma ganin cewa zaman lafiyan ya zama dawamame.

Ya kuma shawarci sauran kasashen duniya da suyi koyi da kasashen Afirka da ke kokarin kawar da afukuwar yaki a nahiyar a shekarar 2020 ta hanyar takaita safarar makamai musamman bindigogi shigowa cikin nahiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel