Takaddamar Maganin Tari: Hukumar NAFDAC ta datse kamfanoni 3 a Kudancin Najeriya

Takaddamar Maganin Tari: Hukumar NAFDAC ta datse kamfanoni 3 a Kudancin Najeriya

Hukumar kula da kafa dokoki akan kayan abinci da magunguna ta Najeriya watau NAFDAC, (National Agency for Food and Drug Administration & Control), ta datse wasu manyan kamfanoni uku na magunguna dake kudancin kasar nan ta Najeriya.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, hukumar ta NAFDAC ta datse kamfanin Peace Standard Pharmac*utical Limited, Bioraj Pharmac*utical Limited da kuma kamfanin Emzor Pharmac*uticals Ind. Ltd sakamakon sanya hannayen su cikin takaddamar maganin nan tari na Codeine.

Mun samu wannan rahoton ne da sanadin shugaba ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, da ta bayyana cikin wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata.

Shugaban Hukumar NAFDAC; Farfesa Mojisola Adeyeye

Shugaban Hukumar NAFDAC; Farfesa Mojisola Adeyeye

Farfesa Adeyeye ta bayyana cewa, wannan hukunci ya zo ne sakamakon binciken da hukumar ta ke gudanarwa na bankado duk wani tuggu da magudi dake tattare da takaddamar maganin Codeine, wanda a halin yanzu gwamnatin tarayya ta hana cinikayyar sa a cikin kasar nan.

KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin Zabe a jihar Ekiti, Jakadun Zabe sun yi arangama

Legit.ng ta fahimci cewa, kamfanonin dake garuruwan Kwara da Legas sun shiga cikin tsaka mai wuya sakamakon dakile masu harkokin masana'antun su yayin bincike da hukumar ta gudanar a ranar 2 ga watan Mayu.

A halin yanzu dai hukumar ta dauki wannan hukunci akan kamfanonin sakamakon rashin hadin kai da suka bayar ga ma'aikatan hukumar da suka hadar har da jami'an tsaro na 'yan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel