Shugaba Buhari ne ya ceto Najeriya daga rugujewa - Keyamo

Shugaba Buhari ne ya ceto Najeriya daga rugujewa - Keyamo

- Fittacen lauya kuma kakakin kungiyar kamfen din shugaba Buhari a 2019, Festus Keyamo ya yabawa shugaban kasar

- Keyamo ya ce hangen nesa da tattalin shugaba Buhari yasa Najeriya bata ruguje bayan 2015

- Keyamo ya ce duk da cewa akwai sauran ayyuka da shugaban bai kammala ba, aikin da ya yi a yanzu kawai ya isa mutane su sake zaben sa

Kakakin kungiyar yakin neman zaben shuguba Buhari a 2019, Festus Keyamo ya ce karbar mulki da shugaba Buhari ya yi bayan zaben 2015 ne ya ceto Najeriya daga rugujewa.

Shugaba Buhari ne ya ceto Najeriya daga rugujewa - Keyamo

Shugaba Buhari ne ya ceto Najeriya daga rugujewa - Keyamo

A wata hira da ya yi a wata shirin talabijin da VinMartin Obiora Ilo, Kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasan ya ce gwamnatin da ta gabata ta Goodluck Jonathan ta riga da dilmiya Najeriya cikin tsaka mai wuya.

KU KARANTA: Tarihi: Ladi Kwali, mace ta daya tilo dake jikin takardar kudin Najeriya

A cewarsa, bayan shugaba Buhari ya karbi ragamar mulki a 2015, ya yi kokari ya magance galibin matsalolin da gwamnatin bayan ta jefa kasar ciki duk da cewa babu wani isashen kudi a baitil malin kasa a wannan lokacin.

Ya cigaba da cewa ko da yake akwai wasu bangarori da gwamnatin na shugaba Buhari bata magance su ba, tayi matukar kokari sosai musamman idan akayi la'akari da cewa babu isasun kudade da za'ayi aiki dasu.

Kalamansa, "Idan ba don hangen nesa da tattali irin na shugaban kasa ba, da tuni Najeriya ta ruguje bayan shekarar 2015. Babu wasu isasun kudade a asusun ajiyar gwamnatin tarayya da za'ayi amfani dashi wajen tafiyar da al'amuran kasar."

A cikin hirar, Keyamo ya ce ayyukan da shugaban kasa yayi zuwa yanzu kawai sun isa mutane su sake zaben sa karo na biyu.

Keyamo ya bayyar da misalan yadda wasu jihohi ke kasa biyan albashin ma'aikatan su har ma gwamnatin baya takan aro kudade kawai don biyan albashi amma a halin yanzu Buhari ya magance wannan matsalolin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel