Hukumar Kwastam ta kama kwatenoni makare da Kwayoyin shaye-shaye

Hukumar Kwastam ta kama kwatenoni makare da Kwayoyin shaye-shaye

- Yaki da shaye-shaye ya samu gagarumar nasara, Kwastam sun dakile yunkurin shigo da muggan kwayoyi

- Kwayoyin dai anyi yunkurin shigo da su ne ta madatsar ruwa ta Tincan Island

Bayanai sun nuna cewa Hukumar hana fasa kauri ta kasa (NCS) reshan jihar Lagos ta Tincan Island ta kame wasu kwantenoni cike da kwayoyin tramadol da aka shigo da su ba tare da izini ba daga kasar Indiya.

Hukumar Kwastam ta kama kwatenoni makare da Kwayoyin shaye-shaye

Hukumar Kwastam ta kama kwatenoni makare da Kwayoyin shaye-shaye

Kame kwayoyin dai ya biyo bayan fashin bakin da masana suke tayi kan illar da kwayoyin ke yiwa Mutane da kuma hana shigowa da kuma sarrafa magungunan da suke dauke da codeine a cikinsu da gwamnatin Najeriya tayi.

Jami'an hukumar hana fasa kauri ne dai su kayi kicibis da kwantenonin a lokacin da ake shirin ficewa da su daga ruwa ba tare da izini ba.

Wani jami'in hukumar da ya bukaci a boye sunan ya shaidawa majiyarmu cewa, kame wadannan kwantenoni ya biyo bayan matsa kaimi da hukumar tayi don magance shigo da kayayyaki ba bisa ka'ida ba.

Amma sai dai har yanzu ba'a kaiga tantance yawan adadin kwayoyin ba a lokacin hada wannan rahoto ba.

Kwayar Tramadol dai Likitoci na bayar da ita ne ga marasa lafiya da suke fuskantar radadi sosai, kuma akwai yiwuwar tun da an hana shigowa da magungunan da suke dauke da codeine a cikinsu masu ta'ammali da kwayoyin zasu koma kan Tramadol.

Ana sa jawabin kakakin hukumar Uche Ejesieme, ya tabbatar da faruwar kame kwantenonin ga majiyarmu. Inda ya ce, da zarar hukumar ta sahihance adadinsu zata sanar da jama'a.

Sai dai kuma yaki bayyana cewa ko sun samu nasarar kama wadansu da ake zargi kayan nasu ne. "Muna dai gudanar da bincike har yanzu, nan da zuwa yammaci zamu bayyana cikakken rahotanmu." A cewar kakakin hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel