Abun da Saraki da Dogara suka tattauna da Buhari bayan sun sa labule jiya

Abun da Saraki da Dogara suka tattauna da Buhari bayan sun sa labule jiya

Kamar dai yadda watakila kuka samu labari cewa a jiya shugaba Muhammadu Buhari ya saka labule da shugabannin majalisar tarayyar Najeriya da suka hada da Honarabul Yakubu Dogara da kuma Sanata Bukola Saraki a fadar sa dake a unguwar Aso Rock, babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai majiyar mu ta labarta mana cewa jim kadan bayan kammala ganawar, shugabannin majalisar sun bayyanawa yan jarida muhimman batutuwan da suka tattauna da shugaban kasar.

Abun da Saraki da Dogara suka tattauna da Buhari bayan sun sa labule jiya

Abun da Saraki da Dogara suka tattauna da Buhari bayan sun sa labule jiya

KU KARANTA: Ayarin Buratai sun yi artabu da yan bindiga a Adamawa

Legit.ng ta samu cewa kamar dai yadda suka labarta, shugabannin majalisar sun kai karar shugaban 'yan sandan Najeriya wurin Buhari din akan yadda yake muzgunawa daya daga cikin su watau Sanata Dino Melaye da kuma batun kasafin kudin shekarar 2018.

A wani labarin kuma, Barikin sojoji ta 16 dake zaman ta a garin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa dake a shiyyar kudu-maso-kudancin kasar nan a jiya mun samu labarin cewa sun ba hamata iska tsakanin sun da jami'an tsaron farar hula.

Kamar dai yadda muka samu duka rigimar ta auku ne sakamakon wata babbar mota shakare da manfetur da jami'an tsaron farar hula na NSCDC suka kama suna kuma kokarin kai ta hedikwatar su kafin daga bisanin sojojin su bukaci kwace motar daga hannun su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel