Tsintsiya ta watse: Dan majalisar tarayya da magoya bayan sa 4,556 sun koma PDP a Kaduna

Tsintsiya ta watse: Dan majalisar tarayya da magoya bayan sa 4,556 sun koma PDP a Kaduna

Dan majalisar tarayya a zauren majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kagarko/Kachia mai suna Honorable Jagaba Adams Jagaba ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar adawa a jihar ta PDP.

Dan majalisar ya sanar da hakan ne a lokacin da aka shirya masa gangamin tarba a ranar Litinin din da ta gabata a garin Zonkwa ta Zangon Kataf tare da dumbin magoya bayan sa da suka kai mutum 4,556.

Tsintsiya ta watse: Dan majalisar tarayya da magoya bayan sa 4,556 sun koma PDP a Kaduna

Tsintsiya ta watse: Dan majalisar tarayya da magoya bayan sa 4,556 sun koma PDP a Kaduna

KU KARANTA: An ba kamfanoni 13 lasislin gina matatar mai

Legit.ng ta samu haka zalika cewa a yayin canza shekar ta sa, tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar PDP a mataki na tarayya Sanata Ahmad Makarfi ya bayyana matukar jin dadin sa game da hakan.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda watakila kuka samu labari cewa a jiya shugaba Muhammadu Buhari ya saka labule da shugabannin majalisar tarayyar Najeriya da suka hada da Honarabul Yakubu Dogara da kuma Sanata Bukola Saraki a fadar sa dake a unguwar Aso Rock, babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai majiyar mu ta labarta mana cewa jim kadan bayan kammala ganawar, shugabannin majalisar sun bayyanawa yan jarida muhimman batutuwan da suka tattauna da shugaban kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel