Shahararren barawon mutanen nan Evans ya koka akan yadda yake rayuwar kunci a kurkuku

Shahararren barawon mutanen nan Evans ya koka akan yadda yake rayuwar kunci a kurkuku

Babban shahararren wanda yanzu haka ake zargi da satar mutanen nan watau Chukwudumeme Onwuamadike da aka fi sani da Evans, a ranar Litinin din da ta gabata ya bayyanawa kotu cikin kuka cewar yana fa rayuwa cikin matsanancin kuci a kurkuku.

Evans wanda yanzu haka yake fuskantar shari'a a gaban babbar kotun tarayya dake a garin Legas ya ayyanawa alkalin cewa yanzu dai masu tsaron sa a gidan yarin suna muzguna masa domin suna barin sa da yunwa.

Haka ma mun samu cewa Evans din wai yace ya gaji da rayuwa cikin kunci yana so ya mutu yanzu.

Shahararren barawon mutanen nan Evans ya koka akan yadda yake rayuwar kunci a kurkuku

Shahararren barawon mutanen nan Evans ya koka akan yadda yake rayuwar kunci a kurkuku

KU KARANTA: Kiristocin Najeriya sun sa kafar wando daya da Buhari

Legit.ng sai dai ta samu cewa ma'aikatan gidan yarin sun musanta zargin sa inda suka ce ba gaskiya bane domin suna bashi kulawa daidai da dukkan sauran yan gidan yarin.

A wani labarin kuma, Barikin sojoji ta 16 dake zaman ta a garin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa dake a shiyyar kudu-maso-kudancin kasar nan a jiya mun samu labarin cewa sun ba hamata iska tsakanin sun da jami'an tsaron farar hula.

Kamar dai yadda muka samu duka rigimar ta auku ne sakamakon wata babbar mota shakare da manfetur da jami'an tsaron farar hula na NSCDC suka kama suna kuma kokarin kai ta hedikwatar su kafin daga bisanin sojojin su bukaci kwace motar daga hannun su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel