Wenger yayi bankwana da Arsenal a jiya

Wenger yayi bankwana da Arsenal a jiya

- Mai horar da wasa na Arsenal, Arsene Wenger, ya yi bankwana da kungiyar cikin yanayi na kewa bayan kammala wasan da Arsenal din ta lallasa kungiyar Burnley da kwallaye 5-0 a filin wasa na Emirates

Wenger yayi bankwana da Arsenal a jiya

Wenger yayi bankwana da Arsenal a jiya

Mai horar da wasa na Arsenal, Arsene Wenger, ya yi bankwana da kungiyar cikin yanayi na kewa bayan kammala wasan da Arsenal din ta lallasa kungiyar Burnley da kwallaye 5-0 a filin wasa na Emirates.

DUBA WANNAN: Majalisa ta amince da kaddamar da kasafin kudin 2018 a makon gobe

Wasan na jiya ya baiwa Arsene Wenger damar samun nasarar jagorantar kungiyar ta Arsenal samun nasara a wasanni 475 daga cikin wasanni 826 da kungiyar ta buga a karkashinsa a gasar Premier.

Wenger ya fara jagorantar Arsenal a wasan farko da ta lallasa kungiyar Blackburn Rovers da kwallaye 2-0 a flin wasa na Ewood Park.

A jimlace cikin cikin shekaru 22 da ya shafe yana horar da Arsenal, Wenger ya jagoranci kungiyar lashe kofunan gasar Premier 3 da kuma kofunan gasar FA 7.

Magoya bayan kungiyar Arsenal ba zasu manta da kakar wasa ta shekarar 2003/2004 ba, lokacin da kungiyar ta kammala baki dayan wasanninta ba tare an samu nasara akanta ba a karkashin mai horarwar Arsene Wenger.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel