Majalisa ta amince da kaddamar da kasafin kudin 2018 a makon gobe

Majalisa ta amince da kaddamar da kasafin kudin 2018 a makon gobe

- Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki da na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara sun bayyana yiwuwar amince wa da kasafin kudi na 2018 nan da makon gobe bayan wata ganawa da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a wannan Litinin

Majalisa ta amince da kaddamar da kasafin kudin 2018 a makon gobe

Majalisa ta amince da kaddamar da kasafin kudin 2018 a makon gobe

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki da na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara sun bayyana yiwuwar amince wa da kasafin kudi na 2018 nan da makon gobe bayan wata ganawa da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a wannan Litinin.

DUBA WANNAN: Turkiyya: Turawa mahaukata ne da suke kira ayi wa Al-Qurani kwaskwarima

Shugabannin biyu sun yi ganawar ta sirri da Buhari a fadarsa ta Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja a wannan Litinin, in da suka shafe tsawon minti 30 suna tattaunawa.

A yayin zantawa da manema labarai bayan ganawar, Saraki ya ce, suna fatan za a kaddamar da kasafin kudin a cikin wannan makon kafin amincewa da shi a makon gobe.

Wannan dai na zuwa ne bayan cika watanni 6 da Buhari ya gabatar da kasafin kudin ga Majalisar kasar, amma har yanzu Majalisar ta kasa amince da shi, lamarin da ya haifar da matsaloli da dama da kuma hana aiwatar da harkokin gwamnati.

Tuni 'yan Najeriya suka fara cece-kuce kan abin da suka kira zagon kasar da Majalisar ke yiwa bangaren zartarwa kamar yadda za ku ji a rahoton da wakilinmu Muhammad Kabir Yusuf ya aiko mana daga Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel