Gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da kashe Falasdiwa 58 da Isra'ila ta yi

Gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da kashe Falasdiwa 58 da Isra'ila ta yi

- Gwamnantin Najeriya ta barranta da goyon bayan kashe-kashen da suke faruwa a Gabas ta tsakiya

- Mutane dai sun tayin cece-kuce kan ko Najeriya ta goyi bayan abin da yake ke faruwa ga Falasdinawan ko kuwa aa

Gwamnatin tarayyar ta yi Allah wadarai da harin da Kasar Isra'ila ta kai kan wadansu masu zanga-zanga kan Falasdinawa har mutane 58 suka rasa rayukansu akan iyakar Gaza a yayin kaddamar da ofishin Jakadancin Amurka.

Gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da kashe Falasdiwa 58 da Isra'ila ta yi

Gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da kashe Falasdiwa 58 da Isra'ila ta yi

Ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta kasa ta bayyana damuwarta da nuna rashin jin dadinta da abinda ya faru ranar ta alhamis.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, ‘ya kamata kasar Isra'ilan ta dakatar da kai hare-hare akan Falasdinawan ba dan komai ba sai dan duba ga wadanda abin ya shafa kananan yara nekuma hakan ya saba da martaba darajar dan Adam da kuma girmama dokar kasa da kasa.

Gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da kashe Falasdiwa 58 da Isra'ila ta yi

Gwamnatin Najeriya tayi Allah wadai da kashe Falasdiwa 58 da Isra'ila ta yi

Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa mutane 58 ne suka rasa rayukansu tare da raunata sama 1000, bayan amfani da karfin tsiya akan iyakar Isra'ila.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar APC a Garin Calabar

Amma hukumomin kasar Isra'ila sun bayyana cewa sun kai wannan hari ne domin dakile wani hari da 'yan kungiyar Hamas su kai kokarin kaiwa kan iyakarta, a cigaba da zanga-zangar nuna adawa ga canjin ofishin jakadancin kasar Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin kudus..

Sojojin kasar Isra'ila sun bayyanawa cewa, Mutane ukun da suka kashe ranar Litinin suna yunkurinsu tada wadansu abubuwa da ake zargin abubuwa masu fashewa ne.

Sojojin kasar Isra'ila sun bayyana cewa mutane sama da 10,000 ne dai suka gudanar da zanga-zanga akan iyakar kasar Isra'ila.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel