Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya gobe ganin Likita

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya gobe ganin Likita

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanawa daukacin al’umman Najeriya cewa zai garzaya kasar Birtaniya gobe Talata, 8 ga watan Mayu domin ganin likitansa amma zai dawo ranan Asabar 12 ga watan Mayu idan Allah ya yarda.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne da daren nan misalin karfe 9 na dare ta shafin sada ra’ayi da zumuntarsa na Facebook dinsa.

Yace: “ Zan tafi kasar Birtaniya gobe domin ganin likita. Zai yi kwanaki 4 kuma ya dawo ranan Asabar, 12 ga watan Mayu.

Fadar shugaban kasa ta saki jawabi akan haka. Zan je jihar Jigawa ranan Litinin da Talata makon gobe idan na dawo.”

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya gobe ganin Likita

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi Birtaniya gobe ganin Likita

Shugaba Buhari ya dawo daga Amurka ranan da yammacin ranan Alhamis, 3 ga watan Mayu, 2018 daga kasar Birtaniya bayan ganawarsa da shugaban kasa Amurka Donald Trump.

Yan Najeriya sun tada jijiyoyin wuya bayan shugaban kasa ya tafi Birtaniya maimakon dawowa gida daga Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel