Kwanan nan zamu garkame shugaban PDP Secondus da abokan badakalar sa - Fadar shugaban kasa

Kwanan nan zamu garkame shugaban PDP Secondus da abokan badakalar sa - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewar nan bada dadewa ba zata garkame shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, tare da ragowar mutanen da suka wawure makudan kudade lokacin mulkin Jonathan.

Fadar shugaban kasar na wadannan kalamai ne a matsayin martani ga wata wasika da jam'iyyar PDP ta aikewa majalisar dinkin duniya tana mai zargin Buhari da almundahana daban-daban.

Mataimakin shugaban kasa na musamman a bangaren yada labarai, Mallam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yau, Litinin, ya zargi jam'iyyar PDP da yin siyasa da gaba tare da neman dawowa gwamnati ta kowacce hanya.

Kwanan nan zamu garkame shugaban PDP Secondus da abokan badakalar sa - Fadar shugaban kasa

Shugaban jam'iyyar PDP; Uche Secondus

Garba Shehu ya bayyana cewar, Secondus, da duk ragowar 'ya'yan jam'iyyar PDP da suka wawure makudan kudade lokacin mulkin jam'iyyar su, zasu gurfana gaban shari'a domin girbar abinda suka shuka.

DUBA WANNAN: Dalibar jami'a a Maiduguri tayi kokarin cusa jaririn da ta haifa cikin masai, kalli hotunan ta'addanci da tayi

Kazalika, ya ce kokarin jam'iyyar PDP na yaudarar majalisar dinkin duniya ba zai samu karbuwa saboda kimar da Buhari keda ita a idon duniya.

Jam'iyyar PDP ta aike da wata wasika zuwa ga ofishin babban sakataren majalisar dinkin duniya tana mai bayyana cewar shugaba Buhari na goyon bayan makiyayan dake kashe mutane a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel