Ka ja kunnen Sifeton Yan Sanda - Saraki da Dogara sun kai karan IGP wajen Buhari

Ka ja kunnen Sifeton Yan Sanda - Saraki da Dogara sun kai karan IGP wajen Buhari

Shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, sun laburatwa shugaba Muhammadu Buhari ya wajabtawa sifeto janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, bin dokan kasa.

Shugabannin majalisan dokokin wadanda sukayi jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawarsu da shugaba Buhari cewa sun nuna rashin amincewarsu da yadda aka ci mutuncin sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, Dino Melaye.

Ka ja kunnen Sifeton Yan Sanda - Saraki da Dogara sun kai karan IGP wajen Buhari

Ka ja kunnen Sifeton Yan Sanda - Saraki da Dogara sun kai karan IGP wajen Buhari

Sun ce abinda sifeto janar na yan sanda yayi na gurfanar da Dino Melaye kan gadon asibiti jahilci ne kuma babu inda za’a gurfanar da mutum ko da dan baranda ne a kan gadon asibiti.

Shugabannin sun baiwa shugaba Buhari tabbacin cewa za su shirya kasafin kudin 2018 a wannan mako.

Kamar yadda muka kawo da safiyar yau cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi wata ganawar gaggawa da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara a yau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel