An kama wata dalibar jami'a na kokarin cusa jaririn da ta haifa cikin masai

An kama wata dalibar jami'a na kokarin cusa jaririn da ta haifa cikin masai

Wata dalibar jami'ar Maiduguri da ba a bayyana sunan ta ba ta kwashi 'yan kallo bayan da aka same ta tana kokarin cusa jaririn da ta haifa cikin masai.

Rahotanni sun bayyana cewar an samu dalibar na kokarin cusa jaririn cikin masan ta karfin tsiya bayan ta kashe shi.

Wasu dalibai dake zaune dakin mata na Murtala dake jami'ar ne suka kama dalibar.

Wani ma'abocin dandalin sada zumunta na Facebook, Simon Ateba, ne ya kwarmata labarin dalibar a shafin sa.

An kama wata dalibar jami'a na kokarin cusa jaririn da ta haifa cikin masai

An kama wata dalibar jami'a na kokarin cusa jaririn da ta haifa cikin masai

Ateba ya nuna bacin ran sa tare da bayyana mamakin sa a kan halin rashin tausayi na wasu mutanen.

Ana yawaita bawa matan dake karatu a manyan makarantu shawarar gujewa fadawa cikin hatsari sakamakon bayar da kan su ga maza.

DUBA WANNAN: Miji ya sheke matar sa saboda bata dafa abinci ba

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, wata mata, Sokari West, ta rasa ran ta sakamakon raunuka da ta samu daga yanka da wuka da mijinta ya yi mata.

Rahotanni sun bayyana cewar, mijin da matar sun kaure da fada ne a gidan su dake Buguma a karamar hukumar Asari-Toru dake jihar Ribas saboda ta ki dafa masa abinci ranar da take farincikin zagayowar ranar haihuwar ta.

Jaridar Daily Sun ta rawaito cewar matar mai shekaru 33 sun fara samun matsala da mijin ta, Ibisaki, a kan batun rashin girka abinci a gidan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel