Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu ya gana da Bukola Saraki da Dogara

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu ya gana da Bukola Saraki da Dogara

Kamar yadda muka kawo da safiyar yau cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi wata ganawar gaggawa da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara a yau.

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu ya gana da Bukola Saraki da Dogara

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu ya gana da Bukola Saraki da Dogara

Shugabannin sun gana da shugaba Muhammadu Buhari ne da ranan nan a fadar shugaban kasa dake Aso Villa, babban birnin tarayya, Abuja.

Ana hasashen cewa shun tattauna ne a kan al'amuran da suka shafi kasafin kudin 2018 wanda bayan watanni 6 gabatar da shi gaban majalisa, har yanzu yan majalisan basu tabbatar da shi ba.

Wannan rashin tabbatarwa ya sabawa manufar fadar shugaban kasa na kawo sauyin kasafin kudin shekara ya dinga farawa da watan Junariu zuwa Disamba na kowani shekara.

KU KARANTA: Buhari zai yi ganawar gaggawa da Saraki, Dogara a yau

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa A yau shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisa, Yakubu Dogara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya kusa da majalisar dokokin kasar tace manyan jami’an majalisar biyu sun samu gayyata daga shugaban kasar domin su gana ba tare da bayyana dalilin ganawar ba.

“Shugaban kasar ya kira shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai domin wata ganawa a yau a fadar shugaban kasa. Ba’a sanar da abunda ganawar zai kunsa ba,” cewar majiyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel