Karancin albashi ya saka ‘yan majalisar Amurka fara kwana a ofis

Karancin albashi ya saka ‘yan majalisar Amurka fara kwana a ofis

- Wasu daga daga cikin ‘yan majalisu a kasar Amurka sun fara kwana a Ofis saboda tsadar rayuwa a birnin Washington DC

- Saidai wasu ‘yan majalisun na son a haramta kwana a ofis saboda, a cewar su, babu girma a cikin hakan sannan zai kawo datti a ginin majalisar

- ‘Yan majalisar kasar Amurka na karbar albashin dalar Amurka $174,000 a shekara, sannan babu kudin alawus din gida

Yawan ‘yan majalisar kasar Amurka dake kwana a ofis, saboda tsadar rayuwa a birnin Washington DC da kuma kudin alawus din gida, na kara yawa.

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan majalisar sun dauki wannan mataki ne domin takaita kasha kudi a muhalli a kwanakin aiki.

Wani dan majalisa, Rap Dan Donovan, ya bayyana cewar yana iya samun dammar yin aiki ne duk da tsadar rayuwa a Washington ta hanyar kwanciya a wani dan siririn lungu a ofishin sa.

Karancin albashi ya saka ‘yan majalisar Amurka fara kwana a ofis

Dan majalisar Amurka ke gyara shimfidar sa domin kwana a ofis

Rayuwa a Washington akwai tsada, idan sai mutum ya mallaki gida a nan kafin ya zama dan majalisa to miloniyoyi ne kawai zasu iya zama wakilan jama’a. Hakan kuma ya saba da tarbiyar da magabata suka dora Amurka a kai.”

DUBA WANNAN: Laifi ne ga Ubangiji ya kasance baka da katin zabe na dun-dun-dun – Babban Fasto Adeboye

Saidai wasu ‘yan majalisar, irin su Bennie Thompson, na son ganin an takawa ‘yan majalisa masu kwana a ofis birki saboda, a cewar sa, hakan zubar da girma ne kuma zai saka majalisar saurin yin datti.

‘Yan majalisa a kasar Amurka na karbar albashin dalar Amurka $174,000 a shekara, albashin da kusan shekaru goma kenan ba a yi kari ba. Mambobin majalisar dattijai a Amurka na karbar albashin $193,400 a shekara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel