Kwankwasiyya sun yi zaben shugabannin APC a Mazabu 406 na Kano

Kwankwasiyya sun yi zaben shugabannin APC a Mazabu 406 na Kano

- Jam’iyyar APC ta gudanar da zaben shugabanni iri biyu a Jihar Kano

- Bangaren Kwankwasiyya da kuma sauran ‘Yan APC sun yi zaben su

- Shugaban Jam’iyyar APC na taware yace za su aikawa APC sunayen

‘Yan bangaren Kwankwasiyya a Jihar Kano sun gudanar da zaben shugabannin Jam’iyyar APC a ware da sauran ‘Yan Jam’iyya kamar yadda labari ya zo mana daga Daily Nigerian a karshen makon nan.

Kwankwasiyya sun yi zaben shugabannin APC a Mazabu 406 na Kano

'Yan Kwankwasiyya kwanaki da su ka fito tarbar gwarzon su

Magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso watau ‘Yan Kwankwasiyya sun yi zaben shugabannin APC a Mazabu 406 da ake da su a Kano inda Shugaban bangaren Jam’iyyar Umar Doguwa ya jagoranta.

KU KARANTA: Kwankwaso ya kauracewa zaben shugabannin APC

Umar Doguwa wanda shi ne Shugaban ‘Yan tawaren Jam’iyyar ya bayyanawa Daily Nigerian cewa sun gudanar da zaben su hankali kwance kuma har Ma’aikatan Hukumar zabe na INEC sun shaida hakan kuma za a aika sunayen ga uwar Jam’iyya.

Bangaren Gwamna mai-ci watau Dr. Abdullahi Umar Ganduje kuma sun yi na su taron ne a lokacin wanda Bashir Karaye da jama’an sa su ka jagoranta. Idan ba ku manta ba a karshen makon nan ne Jam’iyyar APC tayi zaben kananan hukumomin kasar.

Da alama dai zaben na APC ya kara kawo rabuwar kan Jam’iyyar a Kano inda manyan 'Ya 'yan APC irin su Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Kwankwaso da ma Mataimakin Gwamnan Jihar Farfesa Hafiz Abubakar ba su halarci zaben da aka yi Ranar Lahadi ba .

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel