Barayin gwamnati: Osinbajo ya bayyana mutane uku da suka saci $3B a mulkin Jonathan

Barayin gwamnati: Osinbajo ya bayyana mutane uku da suka saci $3B a mulkin Jonathan

- -Jami'iyyar PDP ta kalubalanci mataimakin shugaban kasa da ya bayyana sunayen mutane 3 da suka sace dala biliyan 3 ta gwamnatin tarayya

- An bayyana sunayen wadanda suka saci dala biliyan 3 na rarar kudin danyen mai a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Barayin gwamnati: Osinbajo ya bayyana mutane uku da suka saci $3B a mulkin Jonathan

Barayin gwamnati: Osinbajo ya bayyana mutane uku da suka saci $3B a mulkin Jonathan

A ranar Lahadin nan, 6 ga watan Mayu wani na hannun daman mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Laolu Akande ya bayyana mutanen da ake zargin sun handame dala biliyan uku ta matatar man fetur karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Majiyar mu Legit.ng ta tattaro rahoton da aka bayyana tsohuwar ministan man fetur Diezani Allison Madueke, Jide Omokore da Kola Aluko a matsayin wadanda suka wawure kudin matatar ta man fetur.

DUBA WANNAN: Wani barawo yace ya saci wayoyi sama da 1200 a jihar Legas

Akande yace Diezani, Omokore da Aluko su suka wawure kudin, kuma babu daya daga cikin su da ya fito ya musanta haka.

"Mun san labarin dala biliyan 2.1 na makamai da aka wawure, wannan ma a gwamnatin da ta gabata ne. Mun bayyana sunayen mutanen da aka kama da kudaden da ba a san tushen su ba, ake zargin su da handame kudaden mutane kuma wasu daga cikin su sun dawo da kudaden da basu da cikakken bayanin inda suka samesu. Muna da shaidu da yawa da suke nuna cewa gwamnatin da ta wuce ta daure wa cin hanci da rashawa gindi."

Akande yace sun bayyana sunayen ne domin wasu daga cikin jam'iyyar adawa ta PDP suna son dora wa wasu laifin.

"Kuma duk wani yunkurin kauda hankalin yan Najeriya domin su yarda dasu ba zai yuwu ba. Abun kunya ne ace PDP tana son maida yan Najeriya wawaye, hakan ba zai faru ba."

Kamar yanda majiyar mu Legit.ng ta rawaito a baya, tsohuwar ministan Man fetur, Diezani Allison Madueke, ta zargi hukumar yaki da cin hanci da rashawa na rashin fahimtar kundin tsarin mulkin kasar nan.

Tsohuwar ministan man fetur tayi magana da bakin mataimakin ta, Clem Aguiyi don maida martanin rahoton cewa ta cire Naira biliyan 1.3 daga asusun bankin matatar man fetur a lokacin da take minista.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel