Karshen alewa kasa: Wani makashin Maza ya fuskanci tsattsauran hukuncin Kotu

Karshen alewa kasa: Wani makashin Maza ya fuskanci tsattsauran hukuncin Kotu

Wani Kotun majistri dake jihar Ogun ta yanke ma wani makashin Maza mai shekaru 44, Abiodun Ilesanmi hukuncin zaman gidan Kurkuku a ranar Litinin 7 ga watan Mayu na shekarar 2018, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Alkalin Kotun, G.E Akan ne ya umarci a daure masa Abiodun a gidan Kaso kafin a soma shari’ar ganga ganga, bayan an gurfanar da wanda ake tuhumar da laifin hada baki da wasu miyagun mutane suka kashe matashi.

KU KARANTA: Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai shigar da kara Sajan Chudu Gbesi yana bayyana ma Kotu cewar Abiodun tare da abokansa sun kashe Sunday Adefuoye mai shekaru 25 a ranar 15 ga watan Agusta na shekarar 2015 a unguwar Ijoko dake garin Otta.

Sajan Gbesi ya bayyana laifin nasu a matsayin wanda ya saba ma sashi na 316 da 324 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Ogun na shekarar 2006, ya kara da cewa ABiodun ne ya harba bindigar da ta kashe Mamacin.

Bayan sauraron lauyoyin bangaroi masu kara da masu shigar da kara ne sai Alkali Akan ya umarci a garkame masa Abiodun har zuwa lokacin da babban jami’in shigar da kara na jihar ya bada shawarar yadda za’a tafiyar da shari’ar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Source: Legit

Mailfire view pixel