Tazarcen shugaba Buhari zai cigaba da raba kan ‘yan Najeriya tare da talauta su - PDP

Tazarcen shugaba Buhari zai cigaba da raba kan ‘yan Najeriya tare da talauta su - PDP

- Jam’iyyar PDP tace yunkurin da shugaba Muhammadu Buhari keyi na sake tsayawa takara idan ‘yan Najeriya sun amince, zai kara kawo rarrabuwar kawunan ‘yan Najeriya

- Sakataren jawabai na jam’iyyar Kola Ologbodiyan, ya bayyana cewa mulkin shugaba Buhari na farkon nan a matsayin abun tsoro

- Shugaba Buhari a taron zaben jam’iyyar tasu ta APC, a mazabar Daura dake jihar Katsina, yace sake tsayawarsa takara don jama’ar Najeriya ne

Jam’iyyar PDP tace yunkurin da shugaba Muhammadu Buhari keyi na sake tsayawa takara idan ‘yan Najeriya sun amince, zai kara kawo rarrabuwar kawunan ‘yan Najeriya.

Sakataren jawabai na jam’iyyar Kola Ologbodiyan, ya bayyana cewa mulkin shugaba Buhari na farkon nan a matsayin abun tsoro.

Shugaba Buhari a taron zaben jam’iyyar tasu ta APC, a mazabar Daura dake jihar Katsina, a ranar Asabar, yace sake tsayawarsa takara don jama’ar Najeriya ne.

Tazarcen shugaba Buhari zai cigaba da raba kan ‘yan Najeriya tare da talauta su

Tazarcen shugaba Buhari zai cigaba da raba kan ‘yan Najeriya tare da talauta su

PDP ta bayyana cewa ‘yan Najeriya suna sane da yanda gwamnatin ke mulkin ganganci da wahalar da jama’a, wanda ya haifar da zubar da jini da kuma rarrabuwar kawuna, da kuma kabilanci da wahalar tattalin arziki.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum

Sakamakon haka jam’iyyar ta PDP ta kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da ya nuna daya daga cikin alqawurran da ya daukarwa ‘yan najeriya a shekarar 2015, wanda ya cika.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel