Laifi ne ga Ubangiji ya kasance baka da katin zabe na dun-dun-dun – Babban Fasto Adeboye

Laifi ne ga Ubangiji ya kasance baka da katin zabe na dun-dun-dun – Babban Fasto Adeboye

Babban Faston rukunin Cocinan “Redeemed Christian Church of God” (RCCG), Enoch Adeboye, ya yi kira da babbar murya ga mabiya addinin kirista das u mallaki katin zabe na dun-dun-dun.

Malamin addinin ya bayyana cewar duk Kiristan da bai damu da mallakar katin zaben ba tamakar yana aikata zunubi ne ga Ubangiji.

Fasto Adeboye na wadannan kalamai ne yayin gudanar da addu’o’i na musamman ga mata masu juna biyu, ma’aikatan lafiya da kuma duk masu fama da kalubale a lafiyance.

Laifi ne ga Ubangiji ya kasance baka da katin zabe na dun-dun-dun – Babban Fasto Adeboye

Babban Fasto Adeboye da Shugaba Buhari

A cewar Adeboye, yayin da shekarar babban zaben 2019 ke kara matsowa kusa, dole kiristoci su mallaki katin zabe domin samun dammar zaben shugabannin da zasu sake jagorantar sun a tsawon wasu shekaru hudu.

Ya kara da cewsar, duk da littafin Injila ya bukaci mabiya addinin Kirista da su yiwa shugabanni addu’a ne, kada kuria’a ‘yanci ne na kowanne dan kasa, a saboda haka bai kamata a bar kiristoci a baya ba.

DUBA WANNAN: 2019: Tsohon shugaban kasa Abdulsalam ya bayyana abinda yake bukata daga wurin ‘yan siyasa

Ya yi kira ga mabiyan sa da kada su zabi duk wani shugaba dake daure gindin kashe rai, ko wanene shi tare da bayyana damuwar sa bisa kasha-kashe rayuka a jihar Benuwe da wasu sassa na kasar nan.

Adeboye ya bukaci majalisar kasar das u gaggauta zartar da kasafin kudin shekarar da shugaba Buhari ya mika masu tun karshen shekarar 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel