Dole a daina kisan rashin hankali a kasar nan - Abdulsalami

Dole a daina kisan rashin hankali a kasar nan - Abdulsalami

- Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar yayi kira ga ‘yan Najeriya dasu hada hannu don magance kisan rashin hankali da akeyi fadin kasar nan

- Abdulsalami ya bayyana cewa kisan da akeyi a fadin kasar nan da kuma lalata dukiya da akeyi, ba wani abu bane illa rashin hankali, wanda kuma bashi da wani amfani ga kasar

- Abdulsalami Abubakar ya bayyanawa manema labarai cewa ya zama dole su hada hannu wurin ganin an samar da zaman lafiya a kasar nan

Tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar yayi kira ga ‘yan Najeriya dasu hada hannu don magance kisan rashin hankali da akeyi fadin kasar nan.

Abdulsalami ya bayyana cewa kisan da akeyi a fadin kasar nan da kuma lalata dukiya da akeyi, ba wani abu bane illa rashin hankali, wanda kuma bashi da wani amfani ga kasar.

Abdulsalami Abubakar ya bayyanawa manema labarai, a gidansa na birnin tarayya, cewa ya zama dole su hada hannu wurin ganin an samar da zaman lafiya a kasar nan.

Ya bayyana hakan ne bayan ganawar sirri da ya gamayi da wakilan shuwagabannin arewa da kuma masu fada aji a majalisa (NLSA), wanda ALhaji Tanko Yakasai ya jagoranta.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum

Ya bukaci ‘yan Najeriya dasu san cewa idan babu zaman lafiya to babu kasa, saboda haka ya zama dole su shaidawa jami’an tsaro wadanda ke gudanar da ta’addanci a kasar nan, ba wai a barwa gwamnatin tarayya aikin ba.

A halin da ake ciki, guguwar zaben 2019 na cigaba da karatowa inda yan siyasa ke cigaba da kokarin ganin sun kare kujerunsu ta yadda wani ba zai kwace masu mukamansu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel