Sojoji sun ganawa wani mai cutar asthma da dan uwansa azaba a jihar Legas

Sojoji sun ganawa wani mai cutar asthma da dan uwansa azaba a jihar Legas

- Wasu Sojoji wanda aka bayyana cewa sun gudanar da aiki ne bisa ga umurnin wani mai gidan haya a jihar Legas, sun ganawa mai ciwon asthma azaba a Lekki Palm City Estate dake jihar Legas

- Sojojin su biyar ne wadanda suka shiga estate din tare da mai gidan da kuma mai kula da gidan bayan ‘yar rashin jituwa da suka samu tsakaninsu

- Sojojin sun yiwa mazaunin gidan hayar duka, wanda aka sani da Ayoyemi tare da kaninsa har saida suka suma

Wasu Sojoji wanda aka bayyana cewa sun gudanar da aiki ne bisa ga umurnin wani mai gidan haya a jihar Legas, sun ganawa mai cutar asthma azaba a Lekki Palm City Estate dake jihar Legas.

Sojojin su biyar ne wadanda suka shiga estate din tare da mai gidan da kuma mai kula da gidan bayan ‘yar rashin jituwa da suka samu tsakaninsu da mai gidan.

Sojojin sun yiwa mazaunin gidan hayar duka, wanda aka sani da Ayoyemi tare da kaninsa har saida suka suma, wanda yayi sanadiyar sai da aka kai mai ciwon asthma asibiti, inda ya samu saukin tasowar ciwonsa.

Sojoji sun ganawa wani mai cutar asthma da dan uwansa azaba a jihar Legas

Sojoji sun ganawa wani mai cutar asthma da dan uwansa azaba a jihar Legas

Wani daga cikin mazaunan gidan ya bayyana cewa rikicin ya fara ne lokacin da Ayoyemi, ma’aikacin asibiti ya dawo gidan a watan Maris na 2018, inda Dominic, mai kula da gidajen ya hadashi da mai gidan domin suyi magana a waya bayan y agama biyan kudin gidan.

KU KARANTA KUMA: Kada a kuskura Melaye ya mutu a tsare – Fasehun yayi gargadi

Inda mai gidan ya fada masa cewa baya son matasa su zauna a gidan nasa, wanda hakan ya harzuka Ayoyemi, ya bukaci da a mayar masa da kudinsa wanda mai gidan yaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel