Yanzu yanzu: Jirgin shugaban kasa ya tashi daga Daura ya nufi babban birnin Tarayya Abuja (Hotuna)

Yanzu yanzu: Jirgin shugaban kasa ya tashi daga Daura ya nufi babban birnin Tarayya Abuja (Hotuna)

Da safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi sallama da garin Daura inda ya nufi fadar Aso Rock dake babban birnin Tarayya Abuja, bayan ziyarar kwanaki biyu da ya kai mahaifar tasa.

Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari ya isa garin Daura ne a ranar Asabar, da nufin ya halarci zabukan shuwagabannin jam’iyyar APC a matakin mazaba, inda ya kada kuri’arsa, kuma aka gudanar da zaben aka gama ba tare da wata matsala ba.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Ali Nuhu zai sake shirya Fim din Mujadala don tunawa da Ahmad S Nuhu

Yanzu yanzu: Jirgin shugaban kasa ya tashi daga Daura ya nufi babban birnin Tarayya Abuja (Hotuna)

Buhari

A yayin zaman nasa a garin Daura, shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kungiyar gwamonin jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, da kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdul Azeez Yari.

Gwamnonin biyu sun kai ma shugaba Buhari korafi game da yadda aka samu matsaloli da dama a duk fadin kasar nan a zabukan da APC ta shirya, musamman a garin Fatakwal, inda aka samu rashe rashen rayuka, ko a jihar Anambra ma, sai da ministan Buhari, Ngige ya taka da kafarsa.

Yanzu yanzu: Jirgin shugaban kasa ya tashi daga Daura ya nufi babban birnin Tarayya Abuja (Hotuna)

Buhari

A wani labarin kuma ana sa ran yau, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Jigawa don ganawa da gwamnan jihar tare da al’ummar jihar gabaki daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel