Ba daɗin ji: Motar Tankar Mai da bi ta kan Jaririya

Ba daɗin ji: Motar Tankar Mai da bi ta kan Jaririya

- Mutuwa mai zuwa a yanayi daban-daban, wata jaririya ta gamu da ajalinta yayin da mai Adaidaita sahun da mamata ke ciki yayi yunkurin wuce Direban Tanka

- Lamarin dai ya far Bauchi kuma tuni 'Yan sanda suka cafke Direban Tankar da Mai Adaidaitan

Lamarin ya faru ne a lokacin da direban babur mai kafa 3 yake yunkurin wuce motar tankar mai a daidai shataletalen babban bankin Najeriya wato CBN inda aka yi rashin sa'a jaririyar ta fado daga babur din wanda aka samu akasi tankar man ta bi ta kan yarinyar.

Wani mai magana da manema labarai ya bayyana cewa lokacin da al'amarin ya auku naje shataletalen CBN, wanda a nan ne naga jaririyar kwance a bakin titi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kungiyar gwamnonin APC na kasa

Mataimakin shugaban hukumar kiyaye hadura ta FRSC dake Bauchi Paul Guar, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a yayin da aka zanta shi ta wayar salula, ya kara da cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, wanda wani direban Keke Napep yake yunkurin ba wa babbar motar tazara ta bangaren dama a dai-dai shataletalen.

Ya cigaba da cewa "Direban Keke Napep din yana dauke ne da wata mata a ciki wadda take dauke da jaririyar a hannunta, a yunkurinsa na tserewa motar aka samu akasi ya taba tayar motar wanda hakan ne ya yi sanadin fadowar yarinyar daga babur din wanda motar ta bi ta kanta".

A lokacin da al'marin ya faru an yi gaggauwar kai yarinyar asibiti domin ceto rayuwarta, wanda daga bisani rai ya yi halinsa.

Kakakin hukumar 'Yan sanda ta jihar Bauchi DSP Kamal Abubakar, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.

Ya kuma kara da cewa hukumar ta su ta kama Direban motar da direban Keke Napep din baki dayansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel