Abin tausayi: Yadda jami'an 'Yan sanda biyar suka mutu a hadari sakamakon rashin kyan hanyar Kano-Zaria

Abin tausayi: Yadda jami'an 'Yan sanda biyar suka mutu a hadari sakamakon rashin kyan hanyar Kano-Zaria

- Lalacewar hanyar Kano zuwa Zaria na cigaba da zama sandiyyar ajalin matafiya kusan duk rana

- Yanzu haka dai Titin ya zamo dalilin Mutuwar Dalibai masu karatun aikin na 'Dan sanda har su 6

Wata matsahiyar 'yar sanda Mai suna ASP Aisha Bello tare da abokan aikinta biyar ne suka mutu a wani hadari da ya rutsa da su a hanyar Kano zuwa Zaria sakamakon lalacewar hanyar.

Jami'an yan sanda masu karatun mukamin Assistant Superintendent of Police (ASP), suna karatu ne a jami'ar karatun aikin 'Dan sanda dake garin Wudi a Kano. Kuma sun yi hadarin ne tare da wasu fasinja biyu a cikin Motar.

Abin tausayi: Yadda jami'an 'Yan sanda biyar suka mutu a hadari sakamakon rashin kyan hanyar Kano-Zaria

Abin tausayi: Yadda jami'an 'Yan sanda biyar suka mutu a hadari sakamakon rashin kyan hanyar Kano-Zaria

An dai rawaito cewa, Motar tasu kirar Golf tayi hadari ne tare da wata J5, yayin da daliban 'Yan sandan suke kan hanyarsu ta zuwa hutun tsakiyar zangon karatu.

KU KARANTA: Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum

Titin dai na Kano zuwa Zaria yana yawan lakume rayuka da dama, ya zama tamkar wani tarko ne na Mutuwa, idan har kana kan hanyar to sai dai addu'a.

Aisha Bello dai ita ce shugabar Mata Musulmai a Makarantar, kuma ba kasafai ake samun mayan jami'an 'Yan sanda Musulmai Mata ba. wannan dalili ne yasa Mutuwar tata ya zama abin jimami sosai.

Wani ganau yayin hadari, ya shaidawa majiyarmu cewa, bayan taho mu gama da Motar tayi, sai hayaki ya barke wanda hakan yayi sandiyyar mutuwar jami'an 'yan sandan shida nan take.

Dabiban Jami'an dai an bayyana sunansu da; ASP Aisha Bello mai karatun (Sociology) da ASP Abdulrahman Dari mai karatun (Physics) ASP AM Bello mai karatun (Physics) ASP Yusuf Shehu mai karatun (Sociology) ASP Rufai Dikko mai karatun (Computer Science) APS El-Yaqub.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel