Abunda Buhari ya fada mani dangane da taron APC na kasa - Okorocha

Abunda Buhari ya fada mani dangane da taron APC na kasa - Okorocha

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da gwamna Rochas Okorocha da kuma gwamna Abdulaziz Yari a garin Daura

- Mataimakin shugaban kasa ta fannin sadarwa Bashir Ahmed, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin ciyaman na kungiyar cigaban gwamnoni Rochas Okorocha

- Okorocha ya bayyana cewa ya sanar da shugaban kasar yadda tarurrukan jam’iyyar ta APC ya gudana a fadin kasar, inda ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda wasu ‘yan jam’iyyar suka nuna wata halayya a lokacin taron

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da gwamnonin jihohin Imo, Rochas Okorocha da kuma na Zamfara, Abdulaziz Yari, a garin Daura dake jihar Katsina, a ranar Lahadi.

Mataimakin shugaban kasa ta fannin sadarwa Bashir Ahmed, ya bayyana ta hanyar shafinsa na tuwitta a ranar Lahadi, cewa shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin ciyaman na kungiyar cigaban gwamnoni Rochas Okorocha.

Okorocha ya bayyanawa manema Labarai, cewa ya sanar da shugaban kasar yadda tarurrukan jam’iyyar ta APC ta gudana a fadin kasar, inda ya bayyana rashin jin dadinsa game da yadda wasu ‘yan jam’iyyar suka nuna wata halayya a lokacin taron.

Abunda Buhari ya fada mani dangane da taron APC na kasa - Okorocha

Abunda Buhari ya fada mani dangane da taron APC na kasa - Okorocha

Akan martanin shugaban kasar, gwamnan yace; “Yayi Magana kamar shugaban kasa sannan kuma zai dauki matakan da suka dace domin gyara wannan jam’iyya tamu, APC, ba wai a jihar Imo kadai ba harma a fadin kasar baki daya, domin tabbatar da cewa an girmama damokradiyan cikin gida."

Abdulaziz Yari kuma ya bayyana cewa taron na yankin arewa maso yammacin kasar an gudanar dashi lami lafiya, a bayanan da muke dasu a yanzu wuraren da mutane suka zaci za’a samu rikici kamar jihohin Katsina, Zamfara, Kebbi da kuma Sokoto, yayishi an gam aba tare da wata matsala ba.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum

NAN ta ruwaito cewa an zubar da jini a jihar Delta, a wurin taron, inda har saida jami’an hukumar ‘Yan Sanda ta jihar, ta tabbatar da cewa dan takarar ciyaman ya rasa ransa a karamar hukumar Ughelli ta yammacin jihar.

Idan ba ku manta ba dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai yace ba tarin dukiya ta sa ya shigo siyasa ba inda yace kokarin ganin ya gyara kasar nan ta sa ke neman ya zarce a mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel