Duk wanda bai da katin zabe ba zai shiga coci na ba – Fasto ga masu bauta

Duk wanda bai da katin zabe ba zai shiga coci na ba – Fasto ga masu bauta

Limamin cocin Flock of Christ Mission, Warri, jihar Delta Bishop Simeon Okah ya sanar da cewa daga yanzu, duk wani dan cocinsa da bai mallaki katin zabe ba, “ba za’a bar shi yayi bauta ba.”

Har ila yau Fasto Okah ya kasance shine mataimakin shugaban kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, sannan kuma yayi sanarwar ne yayinda yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Warri, jihar Delta.

Yace zamani ya wuce da kiristoci ke kallon siyasa a matsayin sabo.

Duk wanda bai da katin zabe ba zai shiga coci na ba – Fasto ga masu bauta

Duk wanda bai da katin zabe ba zai shiga coci na ba – Fasto ga masu bauta

Babu shakka yan Najeriya sun dauki al’amarin mallakar katin zabe da muhimmanci a wannan karo, domin a bayyana yadda aka kori ma’aika uku kwanan nan saboda basu da katin zabe.

KU KARANTA KUMA: Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa a yau shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisa, Yakubu Dogara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya kusa da majalisar dokokin kasar tace manyan jami’an majalisar biyu sun samu gayyata daga shugaban kasar domin su gana ba tare da bayyana dalilin ganawar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel