Dalilin da ya sa na bukaci hukuncin kisa kan masu yada kalaman kiyayya – Sanata Sabi

Dalilin da ya sa na bukaci hukuncin kisa kan masu yada kalaman kiyayya – Sanata Sabi

Sanatan da ya gabatar da kudirin neman hukuncin kisa ga masu yada kalaman kiyayya, Sabi Abdullahi ya bayyana hujjarsa na yin haka.

Acewarsa, ya nemi ayi hakan ne ba wai don kawai ya ingiza a sanya wa kafafen yada labarai matsin lamba ba, ko a dakile ‘yancin fadar albarkacin bakin ‘yan Najeriya ba.

Sanata Sabi, dan jam’iyyar APC mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa, yayi karin hasken cewa idan har aka kafa dokar, to ‘yan Najeriya za su kama kan su, ta yadda za a kara samun dankon zumunci tsakanin yankunan kasar nan da junan su wato a zama tsintsiya madaurin ki daya.

Ya kara da cewa kafa dokar zai tsayar da yadda ake yawan dibga kasassaba, katobara, izgilanci da muzanta juna da munanan kalaman da ke iya haddasa mummunan rikici da kashe-kashe mara ma’ana.

Dalilin da ya sa na bukaci hukuncin kisa kan masu yada kalaman kiyayya – Sanata Sabi

Dalilin da ya sa na bukaci hukuncin kisa kan masu yada kalaman kiyayya – Sanata Sabi

Sanatan ya yi wannan jawabi ne a wani taro na Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida na Duniya. Na sheakarar 2018 da Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya shirya.

Ya kara nuna cewa yawan yayata kalaman kiyayya a kasar nan, musamman a wasu kafafen yada labarai na zumunta, abin firgici da kuma tashin hankali ne matuka.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai yi ganawar gaggawa da Saraki, Dogara a yau

Ya ce idan ba a dauki mataki ba, to ya na gudun kada wata rana irin wadannan kalamai su haddasa rikice-rikice, alhali Najeriya babu abin da ta ke bukata kamar zaman lafiya da ingantuwar zamantakewa tsakanin mazauna sassan kasar nan daban-daban.

Idan bai bazaku manta ba Abdullahi ya kasance shi ne Shugaban Kwamitin Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Majalisar Dattawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel