Barayin gwamnati: Secondus ya yiwa EFCC aike

Barayin gwamnati: Secondus ya yiwa EFCC aike

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus ya rubuta wata takarda zuwa ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya (EFCC), Ibrahim Magu, inda yayi mishi bayanin cewar bai kamata sunan shi ya fito a cikin jerin sunayen barayin gwamnati da hukumar ta fitar ba.

Barayin gwamnati: Secondus ya yiwa EFCC aike

Barayin gwamnati: Secondus ya yiwa EFCC aike
Source: Depositphotos

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus ya rubuta wata takarda zuwa ga shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya (EFCC), Ibrahim Magu, inda yayi mishi bayanin cewar bai kamata sunan shi ya fito a cikin jerin sunayen barayin gwamnati da hukumar ta fitar ba.

DUBA WANNAN: 'Yar shekara 19 ta lashe zaben kujerar Kansila

A wata sanarwa da mai magana da yawun shi yayi, Ike Abonyiy, yace Secondus ya bayyana cewar bai karbi makudan kudin da ake zargin shi da cewa ya karba ba, wanda yawan su ya kai naira miliyan 200, daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Sambo Dasuki, kamar dai yanda gwamnatin tarayya ta bayyana.

A wata wasika da Lauyan Secondus din ya fitar a ranar 3 ga watan Mayun nan, Emeka Etiaba (SAN), ya bukaci da a cire sunan Uche Secondus din daga cikin jerin sunayen barayin gwamnati da gwamnatin tarayya ta fitar, sannan kuma ya tura kofi na wasikar zuwa ga Ministan Shari'a Abubakar Malami, da kuma wasu manyan masu fada aji a kasar nan.

Wasikar ta jawo hankalin hukumar ta EFCC inda take bayyana cewar ta riga ta mikawa kotu dukkan lamuran barayin gwamnati, saboda haka kamata yayi suje su kaiwa gwamnati shaidar su basu zo suna ta faman babatu a kafafen yada labarai ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel