'Yar shekara 19 ta lashe zaben kujerar Kansila

'Yar shekara 19 ta lashe zaben kujerar Kansila

Ellie Emberson, matashiya ce mai shekaru 19, kuma tana daya daga cikin masu karancin shekaru da aka zaba a matsayin kansila a kasar Ingila, bayan zaben kananan hukumomi da aka gabatar ranar alhamis dinnan.

DUBA WANNAN: Gaba da gaban ta: ‘Yan fashin da suka tare hanyar Buratai a Adamawa sun ji maza, kalli hotunan su

Emberson, ta lashe zaben kujerar ta kansila a karamar hukumar Readind a karkashin jam'iyyar Labour a gundumar Minster. Kansilan zata rike mukamin har na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Lashe zaben nata ya kawo wanu sauyi a siyasar yankin, domin kuwa yawancin wadanda ake zaba a matsayin kansiloli su kan haura shekaru 60 da haihuwa. Emberson tace tana fatan lashe zaben nata zai bawa matasan yankin damar tashi tsaye wurin shiga harkar siyasa a kasar.

"Matasa suna bukatar wakilci, da akwai matasa a wannan yankin, saboda haka akwai bukatar wani ya shugabance su domin a san irin bukatunsu, shine yasa nace bari na gwada na gani ko zan dace."

Ellie Emberson tace tana fatan samun goyon bayan karamar hukumar wajen samar da wasu shirye-shirye da zasu taimakawa matasa, kuma za tayi aiki da jam'iyyarta ta Labour domin cimma burinta na samar da gidaje ga matasan yankin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel