Buhari zai yi ganawar gaggawa da Saraki, Dogara a yau

Buhari zai yi ganawar gaggawa da Saraki, Dogara a yau

A yau shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisa, Yakubu Dogara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wata majiya kusa da majalisar dokokin kasar tace manyan jami’an majalisar biyu sun samu gayyata daga shugaban kasar domin su gana ba tare da bayyana dalilin ganawar ba.

“Shugaban kasar ya kira shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai domin wata ganawa a yau a fadar shugaban kasa. Ba’a sanar da abunda ganawar zai kunsa ba,” cewar majiyar.

Buhari zai yi ganawar gaggawa da Saraki, Dogara a yau

Buhari zai yi ganawar gaggawa da Saraki, Dogara a yau

Haduwar shugaban kasa tare da Saraki da Dogara na zuwa ne a daidai lokacin day an majalisa ke kira ga tsige shugaban kasar sakamakon siyan jirgin yaki da yayi kan $496m ba tare da yardan majalisar ba.

Yan majalisa masu adawa da wannan lamari daga bangarorin biyu sunyi kira ga tsige shugaban kasar saboda rashin neman yardarm su.

KU KARANTA KUMA: Idan aka same ni da laifi zan ajiye aiki in mika kai na gaban EFCC – Inji mai ba Buhari shawara

Idan ba ku manta ba dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai yace ba tarin dukiya ta sa ya shigo siyasa ba inda yace kokarin ganin ya gyara kasar nan ta sa ke neman ya zarce a mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel