Idan aka same ni da laifi zan ajiye aiki in mika kai na gaban EFCC – Inji mai ba Buhari shawara

Idan aka same ni da laifi zan ajiye aiki in mika kai na gaban EFCC – Inji mai ba Buhari shawara

- Wani daga cikin masu ba Gwamnatin Shugaba Buhari yace zai yi murabus

- Bashir Ahmad zai ajiye aiki ne amma fa idan an same shi da rashin gaskiya

- Wata Baiwar Allah dai ta zargi na-kusa da Shugaba Buhari da satar dukiya

Jiya ne mu ka ji cewa daya daga cikin Hadiman Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna Bashir Ahmad yayi alkawarin ajiye aikin sa idan har ta tabbata an same shi da laifin rashin gaskiya.

Idan aka same ni da laifi zan ajiye aiki in mika kai na gaban EFCC – Inji mai ba Buhari shawara

Bashir Ahmad yace wadanda su ka zagaye Buhari ba barayi bane

Bashir Ahmad wanda yana cikin masu ba Shugaban kasar shawara a kafafen sadarwa na zamani yayi wannan magana ne a shafin sa na Tuwita inda yake maida martani ga wata Baiwar Allah ta zargi na kusa da Shugaban kasar da sata.

Wannan Baiwar Allah mai suna Fakhuus Hashim tace wadanda su ka zagaye Shugaban kasa Muhammadu Buhari satar dukiyar kasar nan kurum su ke yi. Sai dai Hadimin Shugaban kasar ya nemi ta kawo hujja inda yace a fara ta kan sa.

KU KARANTA: Kashe-kashe: Ghali Na’abba yayi kaca-kaca da Shugaba Buhari

Malam Bashir yace da zarar aka kawo wata hujja da ta nuna cewa ya aikata rashin gaskiya zai yi murabus daga ofishin na sa sannan ya mika kan sa a gaban Hukumar EFCC mai yi wa masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa babu wata-wata.

Idan ba ku manta ba dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai yace ba tarin dukiya ta sa ya shigo siyasa ba inda yace kokarin ganin ya gyara kasar nan ta sa ke neman ya zarce a mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel