Za mu kawo karshen wahalar da Buhari ya jefa jama’a – Secondus

Za mu kawo karshen wahalar da Buhari ya jefa jama’a – Secondus

- Jam’iyyar PDP tace za ta kifar da Gwamnatin Shugaba Buhari

- Shugaban Jam’iyyar PDP yace APC ta jefa jama’an cikin wahala

- Secondus ya jagoranci wani babban gangami a Kudancin kasar

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ya bayyana cewa Jam’iyyar su za ta ceci ‘Yan Najeriya daga mulkin APC. Secondus ya bayyana wannan ne a karshen makon da ya wuce a Garin Osun.

Za mu kawo karshen wahalar da Buhari ya jefa jama’a – Secondus

Uche Secondus yace Buhari ya jefa mutane cikin wahala

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa a Ranar Asabar, Jam’iyyar PDP ta gudanar da wani gangami na Yankin Kudu-maso-yammacin Kasar a filin shakatawan Nelson Mandela da ke Garin Osogbo a Jihar Osun.

KU KARANTA: An kashe wani wajen babban taron Jam'iyyar APC

Dubban ‘Yan PDP irin su tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, da Gwamna Ayo Fayose da tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido, da wasu manyan PDP a Yankin irin su Rasheed Ladojo su na wajen taron.

Uche Secondus yace Jam’iyyar adawar za ta kawo karshen wahalar da Gwamnatin Buhari ta jefa jama’a a Kasar. Wani ‘Dan takarar Gwamnan Osun Oluomo Gbenga Owolabi ya sha alwashin Jam’iyyar sa za tayi nasara a zaben Gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel