PVC: Gwamnan Gombe ya nemi Davido yayi waka ta musamman kan zaben 2019

PVC: Gwamnan Gombe ya nemi Davido yayi waka ta musamman kan zaben 2019

- Gwamnan Gombe ya nemi Davido ya rangada waka game da 2019

- Dankwambo yace zai so ayi kira ga ‘Yan kasa su nemi katin zabe

- Gwarzon Mawakin yace ya yarda ya rera waka domin cigaban kasa

Mun samu labari cewa a makon can ne wani babban Gwamnan PDP a Arewacin Najeriya ya nemi alfarma wajen fitaccen Mawakin nan na Najeriya da aka sani da Davido wanda shi kuma ya amince ya yarda da abin da aka nema.

PVC: Gwamnan Gombe ya nemi Davido yayi waka na musamman kan zaben 2019

Gwamna Dankwambo ya nemi Davido yayi waka kan zabe

Mai Girma Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na Jihar Gombe yayi kira ga Davido wanda yake tashe a Duniya cewa yayi amfani da basirar da Allah ya ba sa domin yayi kira ga Jama’an Najeriya su karbi katin zabe mai zuwa.

Gwamna Ibrahim Dankwambo ya roki Davido yayi wata waka da za ta sa jama’a su yanki katin zabe na PVC domin ganin kowa ya kada kuri’a a zaben 2019. Gwamnan yace yana cikin masoya wannan shararren Mawakin.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa mu ka ki marawa Buhari baya - Dattawan Arewa

Shi dai Davido tuni ya amsa wannan kira inda yace zai yi wannan waka domin ganin ya fadakar da jama’a game da karben katin na PVC. Duk an yi wannan ne a shafin Tuwita inda Davido yace zai yi abin da zai taimaki kasar sa.

Ku na da labari cewa Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayyar kasar ta aminta da ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC saboda ba barayi bane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel