Yanzu babu karamar Hukumar da ba ta iya biyan albashi a Kaduna – El-Rufai

Yanzu babu karamar Hukumar da ba ta iya biyan albashi a Kaduna – El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai yayi wani jawabi yayin da ake shirin zaben kananan Hukumomin Jihar Kaduna inda ya bayyana kokarin da Gwamnatin sa tayi a kan karagar mulki.

Gwamna Nasir El-Rufai lokacin da yake jawabi na yakin neman zabe domin ganin jama’a sun fito sun dangwalawa Jam’iyyar APC a zaben kananan Hukumomin da za ayi a makon gobe ya jero irin cigaban da aka samu a Gwamnatin sa.

Yanzu babu karamar Hukumar da ba ta iya biyan albashi a Kaduna – El-Rufai

Gwamnan Kaduna yace za su yi zabe na adalci a makon gobe

Nasir El-Rufai yake cewa daga hawan su mulki zuwa yanzu babu karamar Hukumar da ba za ta iya biyan albashi ba cikin kananan Hukumomi 23 na Jihar, wanda a da dai sai wasu kananan Hukumomin sun dafawa wasu duk wata.

KU KARANTA: Matan da ke shirin ba maza mamaki a zabe mai zuwa

Hakan ya yiwu ne bayan an kori Ma’aikatan da ba a bukatan su an kuma cire Ma’aikatan bogi. Gwamnan yace kuma za su dauki kwararrun Ma’aikata na Lauyoyi da Injiniyoyi da sauransu domin inganta aikin kananan Hukumomin Jihar.

Gwamna na Kaduna yayi alkawarin gudanar da zabe mai inganci wanda shi ne karon farko da za ayi amfani da na’urar zamani wajen kada kuri’a. Gwamnan yace ba za su yi irin zaluncin PDP ba saboda sun sa Ubangiji ne ke bada mulki ba kowa ba.

Kun samu labari cewa a makon can ne dai Gwamnan na Kaduna ya fita kamfe inda ya tsinewa Sanatocin Jihar albarka a bainar jama’a a dalilin kin amincewa da ba Jihar ba shi da su kayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel