Jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC sun kauracewa taron zabukan jam'iyyar, An kashe mutum guda

Jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC sun kauracewa taron zabukan jam'iyyar, An kashe mutum guda

Rigingimu a cikin gidan jam'iyyar APC a fadin kasar nan sun kara yin zafi a tsakanin jiya da yau.

Zaben fitar da takarar gwamna a jihar Ekiti ya kare da rikici bayan da wasu 'yan daba suka lalata kayan zabe tare da ragargazar magoya bayan wani dan takara.

A jihar Edo, shugaba jam'iyyar APC mai barin gado, Cif Odigie-Oyegun bai halarci wurin zabukan ba kamar yadda Kwankwaso da Dogara suka kauracewa wurin zabukan a jihohin su na Kano da Bauchi.

Jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC sun kauracewa taron zabukan jam'iyyar, An kashe mutum guda

Jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC sun kauracewa taron zabukan jam'iyyar, An kashe mutum guda

A yayin da zabukan aka gudanar da su lami lafiya a jihohin Edo, Bayelsa, Taraba, Kwara da Katsina da sauran su, labarin ba haka yake ba a jihohin Akwa Ibom,Ribas, Oyo, da kuma Delta inda rikici ya dabaibaye batun zabukan.

DUBA WANNAN: Jihar Katsina tayi rashin babban Malamin addinin Islama

A jihar Delta an kashe wani dan takarar neman zama shugaban jam'iyyar a mazaba ta 1o dake Otu-Jeremi a karamar hukumar Ughelli ta kudu ta hanyar daba masa wuka bayan rikici ya barke yayin gudanar da zabukan.

A wasu jihohin da suka hada da Imo, Kano, da Ribas an samu rabuwar kayuwa tsakanin wasu jiga-jigan jam'iyyar da ta kai an samu wurare fiye da daya da ake zabukan shugabannin mazabu na jam'iiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel