‘Yan Jam’iyyar APC ba barayin dukiyar kasa ba ne – Inji Osinbajo

‘Yan Jam’iyyar APC ba barayin dukiyar kasa ba ne – Inji Osinbajo

- Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo yayi yabi Jam'iyyar APC

- Osinbajo yace 'Ya 'Yan APC gyara su ka sa gaba ba ba wai sata ba

- Farfesan yace Jama’an kasar za su amfana da Gwamnatin Buhari

Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayyar kasar ta aminta da ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC mai mulki saboda ba barayi bane. Yace kuma za a ga amfanin Gwamnatin APC.

‘Yan Jam’iyyar APC ba barayin dukiyar kasa ba ne – Inji Osinbajo

Osinbajo yace 'Yan APC aiki ya dame su ba sata ba

Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana wannan ne a wajen zaben Shugabannin Jam’iyyar ta APC da aka shirya a fadin kasar. A Ranar Asabar dinnan da ta gabata Osinbajo yana gundumar sa a Eti Osa da ke cikin Garin Legas,

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai bambanci tsakanin ‘Ya ‘yan APC da wadanda ba su ba, inda yake cewa ba a san ‘Yan APC da wawushe dukiyar al’umma ba. Osinbajo yace aiki kurum ke gaban APC ba satan dukiyar kasar ba.

KU KARANTA: Tsantsagoron kawo gyara a Najeriya ya sa na ke neman zaracewa – Buhari

Yemi Osinbajo yake cewa duk da farashin gangar ‘danyen man fetur ya karye a Duniya bayan hawan Gwamnatin Buhari amma sun yi kokari wajen ganin an yi wa al’ummar Najeriya aiki yana cewa za kuma a cigaba da gyara kasar.

Osinbajo yayi alkawarin cewa Najeriya za ta gyaru a Gwamnatin nan kuma kowa zai amfana. Hakan dai ya zo daidai da jawabin da Shugaban kasa Buhari yayi a Daura inda yace kokarin gyaran kasa ta sa yake neman ya zarce ba komai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel