Abin da ya sa Gwamnatin Buhari ta gaza maganin kashe-kashe – Na’abba

Abin da ya sa Gwamnatin Buhari ta gaza maganin kashe-kashe – Na’abba

- Hon. Ghali Umar Na’abba ya soki Gwamnatin Shugaba Buhari

- Tsohon ‘Dan Majalisar kasar yace Gwamnatin nan na da nawa

- Umar yake cewa Shugaban kasa Buhari ya tsuke kan sa da yawa

A jiya mu ka samu labari cewa Ghali Umar Na’abba wanda tsohon Shugaban Majalisar kasar nan ne ya koka da kashe-kashen da ke faruwa a Najeriya inda yace ya nuna cewa babu Gwamnati a kasar.

Abin da ya sa Gwamnatin Buhari ta gaza maganin kashe-kashe – Na’abba

Ghali Na'abba yace Buhari ba zai iya yaki shi kadai ba

Ghali Umar Na’abba yace abin da ke faruwa na kisan Jama’a bai dace ba. Tsohon Shugaban Majalisar kasar yace Gwamnatin Buhari ta gaza kawo karshen ta’adin ne saboda ba ta da sauri wajen daukar mataki.

KU KARANTA: Atiku Abubakar zai fafata da Buhari a zaben 2019

Tsohon ‘Dan Majalisar yace kisan mutum sama da 30 zuwa 50 ya wuce kima kuma abin Allah wadai ne. Rt. Hon. Ghali Umar Na’abba yace Shugaba Buhari yana ikirarin ya fi kowa sanin abin da yake a kaf kasar.

Babban ‘Dan Majalisar yake cewa Shugaba Buhari ya tsuke kan sa don haka ake samun matsala a kasar. Na’abba yace Buhari bai bada damar daukar shawara daga sauran Jama’a ba kuma ba zai iya mulki shi kadai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel