Kotun daukaka kara ta kwace gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

Kotun daukaka kara ta kwace gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

Wata kotun gwamnatin tarayya da ke zaman ta a garin Legas a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayar da da umurnin mallakawa gwamnatin tarayya wasu manyan gidajen alfarma guda biyu mallakin wasu manyan jami'an sojin ruwan Najeriya Kaftin Olotu Morakinyo da kuma Kaftin Ebony Aneke.

Alkalin kotun, mai shari'a Muslim Hassan shine ya yanke wannan hukuncin biyo bayan karar da hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta shigar a gaban sa.

Kotun daukaka kara ta kwace gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

Kotun daukaka kara ta kwace gidaje 2 da Naira milliyan 11 na manyan sojojin ruwan Najeriya

Legit.ng ta samu haka zalika cewa kotun ta kuma mallakawa gwamnatin tarayyar makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 11 da ake kyautata zaton mallkakar Kaftin Aneke ne.

A wani labarin kuma, Labarin da muka samu daga majiyar mu ta DailyTrust ta bayyana mana cewa a jiya ne dai fitaccen dan siyasar nan kuma shugaban karamar hukumar Kuje dake a birnin tarayya Abuja Alhaji Abdullahi D. Galadima tare da mataimakin sa Mista Samuel Tanko sun sha da kyar a hannun mafusatan matasa.

Kamar dai yadda muka samu mafusatan matasan sun yi kukan kura sun afkawa shugabannin karamar hukumar ne biyo bayan nuna goyon bayan su ga takarar tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel