Zaben 2019: Makafi, guragu sauran masu nakasa za su yi zabe - INEC

Zaben 2019: Makafi, guragu sauran masu nakasa za su yi zabe - INEC

Hukumar nan mai zaman kanta ta gwamnatin tarayyar Najeriya da ke da alhakin gudanar da zabe watau Independent National Electoral Commission, INEC ta ayyana cewa dukkan makafi, guragu da saunar masu nakasa za su gudanar da zabe a shekarar 2019 mai zuwa.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ansa tambayoyi daga mahalarta taron karawa juna sani game da muhimmancin yin rijistar zabe a jami'ar garin Abuja.

Zaben 2019: Makafi, guragu sauran masu nakasa za su yi zabe - INEC

Zaben 2019: Makafi, guragu sauran masu nakasa za su yi zabe - INEC

KU KARANTA: Ayarin Buratai sun yi artabu da 'yan bindiga a Adamawa

Legit.ng ta samu cewa Farfesa Yakoob ya kuma kara da cewa tuni dai hukumar ta kammala shire-shiren don tabbatar da hakan sannan kuma ya shawarci dukkan wanda bai yi rijistar ba kuma ya kai shekaru 18 da haihuwa da ya je yayi.

A wani labarin kuma, Majalisar wakilai a tarayyar Najeriya ta ayyana cewa ta kammala shire-shiren zartas da kasafin kudin shekarar 2018 a matsayin doka a cikin sati mai kamawa kamar dai yada Honorable Abdulrazaq Namdas da ke zaman mai magana da yawun majalisar ya fadawa manema labarai a jiya.

A cewar Abdulrazaq Namdas 'yan majalisar sun dauki kasafin kudin da muhimmacin gaske shi ya sa ma suka hanzarta kammala aiki kan sa kuma suke shirin kai shi a zauren ranar Talata mai zuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel