An bai wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

An bai wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba wa wasu kamfanoni akalla 13 lasisin samun damar gina kananun matatun mai a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur dake kudu maso kudancin Najeriya.

Mun samu cewa kimanin kamfanoni 35 ne dai suka nemi lasisin sai dai amma 13 ne kadai suka samu lasisin na gina matatun bayan kammala sharuddan da aka gindaya masu.

An bai wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

An bai wa kamfanoni 13 lasisin kafa kananan matatun man fetur

Legit.ng ta samu cewa da yake karin bayani, shugaban hukumar rukunin kamfanonin NNPC na Kasa, Mista Maikanti Baru ya bayyana cewa hukumar ta bi dukkan dokoki wajen bayar da lasisin.

A wani labarin kuma, Babbar hadaddiyar kungiyar Kiristocin Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN ta sha alwashin cigaba da yi wa gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari zanga-zangar kin jini a harabar majami'un su a dukkan fadin kasar nan.

Wannan dai bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar a wata fira da yayi da wakilin majiyar mu inda ya bayyana cewa kiristocin kasar nan sun gaji da yadda jami'an tsaro ke yi wa matsalar rashin tsaro rikon sakainar kashi suna bari ana kashe su kamar kaji a wuraren ibadar su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel