Fitaccen dan siyasa ya sha da kyar bayan ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

Fitaccen dan siyasa ya sha da kyar bayan ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

Labarin da muka samu daga majiyar mu ta DailyTrust ta bayyana mana cewa a jiya ne dai fitaccen dan siyasar nan kuma shugaban karamar hukumar Kuje dake a birnin tarayya Abuja Alhaji Abdullahi D. Galadima tare da mataimakin sa Mista Samuel Tanko sun sha da kyar a hannun mafusatan matasa.

Kamar dai yadda muka samu mafusatan matasan sun yi kukan kura sun afkawa shugabannin karamar hukumar ne biyo bayan nuna goyon bayan su ga takarar tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Fitaccen dan siyasa ya sha da kyar bayan ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

Fitaccen dan siyasa ya sha da kyar bayan ya nuna goyon bayan sa ga tazarcen Buhari

KU KARANTA: Buhari sai ya riga rana faduwa a 2019 - Babban malamin addini

Legit.ng ta samu cewa matasan dai sun farwa shugabannin karamar hukumar ne yayin da suke fita daga dakin taro jim kadan bayan kammala tattaunawar su da sauran jiga-jigan jam'iyyar masu rike da mukamai.

A wani labarin kuma, Haddadiyar hadakar nan ta tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo da ta kuduri aniyar fatattakar shugaba Muhammadu Buhari daga mulki a zaben 2019 mai zuwa ta shirya tsaf domin ayyana jam'iyyar da za su goya wa baya.

Wannan matakin dai da hadakar ta dauka kamar yadda muka samu, ya biyo bayan kasa cimma daidaito da jam'iyyar SDP da Cif Obasanjo din ya nemi a yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel