Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta shirya ayyana jam'iyyar da zata goya ma baya

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta shirya ayyana jam'iyyar da zata goya ma baya

Haddadiyar hadakar nan ta tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo da ta kuduri aniyar fatattakar shugaba Muhammadu Buhari daga mulki a zaben 2019 mai zuwa ta shirya tsaf domin ayyana jam'iyyar da za su goya wa baya.

Wannan matakin dai da hadakar ta dauka kamar yadda muka samu, ya biyo bayan kasa cimma daidaito da jam'iyyar SDP da Cif Obasanjo din ya nemi a yi.

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta shirya ayyana jam'iyyar da zata goya ma baya

Hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta shirya ayyana jam'iyyar da zata goya ma baya

Legit.ng ta samu cewa cikin jiga-jigan da yanzu haka ke jan ragamar sabuwar hadakar da kuma suka halarci zaman ta da ya gabata sun hada da tsohon gwamnan jihar Osun Prince Olagunsoye Oyinlola.

Sauran sun hada da Dr. Olisa Agbakoba (SAN) da Dr. Abdujalil Tafawa-Balewa; tare kuma da tsohon shugaban hukumar gyaran dabi'ar 'yan kasa Idi Faruk.

A wani labarin kuma, Babbar hadaddiyar kungiyar Kiristocin Najeriya watau Christian Association of Nigeria, CAN ta sha alwashin cigaba da yi wa gwamnatin tarayya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari zanga-zangar kin jini a harabar majami'un su a dukkan fadin kasar nan.

Wannan dai bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar a wata fira da yayi da wakilin majiyar mu inda ya bayyana cewa kiristocin kasar nan sun gaji da yadda jami'an tsaro ke yi wa matsalar rashin tsaro rikon sakainar kashi suna bari ana kashe su kamar kaji a wuraren ibadar su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel