Da dumin sa: An kashe mutane 27 a harin Gwaska a jihar Kaduna

Da dumin sa: An kashe mutane 27 a harin Gwaska a jihar Kaduna

A kalla mutane 27 ne rahotanni suka bayyana cewar sun mutu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari garin Gwaska dake karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Harin na zuwa ne cikin kasa da sati guda da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan masu hakar ma'adanai a kauyen Janruwa dake karamar hukumar ta Birnin Gwari.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar 'yan bindigar da suka fito daga makwabtan kauyuka dake jihar Zamfara, sun kewaye kauyen Gwaska da Kuiga da misalin karfe 2:3 na ranar jiya, Asabar, 5 ga watan Mayu, tare da yin harbin kan mai-uwa da wabi.

Sun kashe mutane da dama da suka hada da kananan yara tare da kone kauyen mai yawan jama'a 3,ooo. Da yawan mutanen kauyen na zaman gudun hijira a garin Doka mai makwabtaka da su.

Da dumin sa: An kashe mutane 27 a harin Gwaska a jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna; Nasir El-Rufa'i

Wata kungiya mai fafutikar samar da zaman lafiya a karamar hukumar ta Birnin Gwari ta ce mafi yawan wadanda aka kashe din 'yan kungiyar bijilanti ne dake kare jama'ar yankin.

Kungiyar ta ce adadin Wadanda suka mutu zai iya karuwa tare da alkawarin hada gangami domin zuwa dauke gawarwakin mutanen da suka mutu.

DUBA WANNAN: Sojojin Najeriya sun fatattaki makiyayan da suka kai hari Guma bayan ziyarar Buratai

"Muna rokon hukumomi da su dauki matakan gaggawa domin kawo karshen aiyukan ta'addanci dake barazanar share al'ummar Birnin Gwari," in ji kungiyar.

Majiyar jaridar Daily Trust da ta bukaciaci a boye sunanta ta tabbatar da kai harin tare da bayyana cewar maharan sun shigo garin daga jihar Zamfara.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna, S Mukhtar Aliyu, bai amsa ko dawo da kiran da jaridar Daily Trust ta ce tayi masa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel