Sojojin Najeriya sun fatattaki makiyayan da suka kai hari Guma bayan ziyarar Buratai

Sojojin Najeriya sun fatattaki makiyayan da suka kai hari Guma bayan ziyarar Buratai

Cikin kasa da sa'o'i 48 bayan ziyarar da shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya kai karamar hukumar Guma a jihar Benuwe, wasu 'yan bindiga sun kai hari garin.

Buratai ya kai ziyara karamar hukumar ta Guma ne domin ganin halin da jama'a ke ciki da kuma matakan tsaro da aka dauka a karamar hukumar bayan ta sha fama da hare-haren makiyaya.

Wani shaidar gani da ido ya ce wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Guma da yammacin ranar juma'a tare da yin harbin kan mai-uwa da wabi.

Sojojin Najeriya sun fatattaki makiyayan da suka kai hari Guma bayan ziyarar Buratai

Sojojin Najeriya sun fatattaki makiyayan da suka kai hari Guma bayan ziyarar Buratai

"Sun zo sun bude wuta a kan jama'a da yammacin ranar Juma'a. Daga inda muke a garin Gbajimba (shelkwatar karamar hukumar Guma) muna jin karar harbin bindigogin su.

"Jama'a sun shiga firgici tare da gudun fara neman mafaka a kauyuka mafi kusa da su.

DUBA WANNAN: Gasar harbi a hukumar soji: Mace ta bawa maza mamaki

"Bada dadewa ba sai ga shi Allah ya kawo sojoji kuma take suka fara musayar wuta da 'yan bindigar kafin su gudu bayan sun ga dakarun sojin sun fi karfin su."

Da yake tabbatar da faruwar kai harin, shugaban karamar hukumar Guma, Mista Anthony Shawon, ya ce dakarun soji, sun dakile harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel