2019: Ba dukiyar al’umma na ke nema ba inji Shugaban kasa Buhari

2019: Ba dukiyar al’umma na ke nema ba inji Shugaban kasa Buhari

- Shugaba Buhari ya abin da ya sa yake neman ya zarce a mulki a 2019

- Shugaban kasar yace gyara yake son yi a Najeriya ba satar dukiya ba

- Yace tun da ya shigo siyasa dai ba abin da zai samu ya ke dubawa ba

Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yake wajen zaben Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a Garin Daura a Jihar Katsina yayi magana game da shirin da yake na sake neman takara a 2019 da kuma abin da ya sa ya ke neman mulki tun 2003.

Shugaban kasar ya bayyana cewa yana neman sake tsayawa zabe ne domin inganta rayuwar talakawa. Shugaba Buhari yace ba tara abin Duniya ta sa ya ke kokarin ya zarce a kan mulki ba inji mai magana da yawun Shugaban watau Garba Shehu.

Malam Garba Shehu ya fitar da jawabin da Shugaban kasar yayi wajen zaben Shugabannin APC na Kananan Hukumomi. Shugaban kasar yace saboda ya ga an samu canji a rayuwar al’umma ta sa ya fara tsayawa takara tun daga 2003 kawo yau.

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban kasa ya isa Kauyen sa domin zabe

Shugaba Buhari yake cewa ba domin ya tara dukiya yake neman a kara zaben sa a karo na biyu ba. Shugaban kasar ya kuma ce tuni Gwamnatin sa ta fara samun nasarar yin adalci da yin gaskiya tsakanin al’ummar kasar duk da matsalolin da aka samu.

Dazu kun ji cewa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi magana game da Maigidan sa Marigayi Ummaru Musa ‘Yaradua wanda a jiya yayi shekaru 8 da rasuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel